1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta gamsu da rangadin kasashen Larabawa da ta yi

February 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuSH
SGJ Angela Merkel ta ce ta gamsu da rangadin kwanaki 4 data kaiwa kasashen yankin GTT. Merkel ta ce ta gano cewa dukkan sassan da ta tattauna da su sun nuna shirin yin aiki tare don gano bakin zaren warware rikicin yankin GTT. Ko da yake ta nuna damuwa gameda shirin nukiliyar Iran to amma ta ce kofa a bude take don tattaunawa da hukumomin birnin Teheran. Merkel wadda ta kai ziyara a Kuwaiti jiya talata a mataki na karshe na wannan rangadi ta ce maganar daukar matakan soji kan Iran ba ta taso ba. An ba wa Iran dai wa´adin zuwa ranar 21 ga watannan na fabrairu da ta dakatar da shirin sarrafa sinadarin uranium ko kuma kwamitin sulhun MDD ya kakaba mata takunkumi.