Angela Merkel ta fara tattaunawa da shugabannin China | Labarai | DW | 22.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel ta fara tattaunawa da shugabannin China

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta fara ziyarar aiki a kasar Sin wato China a jiya lahadi, a yau ta gana da FM Wen Jiabao lokacin karin kumallo a birnin Beijing. Fm Wen ya tabbatar da cewa kasar sa zata ci-gaba da kare kadarorin Jamus, to amma ya ce ko da yake har yanzu akwai matsaloli a wannan fannin, to amma duk da haka hukuma zata kara matsa kaimi don ganin an cimma nasara. Merkel ta ce ta tabo batun kare hakin bil Adama a China da ma a wasu kasashe daban, inda ta jaddada muhimmancin kare hakin dan Adam. Bayan tattaunawar shugabannin biyu sun sanya hannu kan jerin yarjeniyoyi guda 19 ciki har da kwangilar samar da kanukan jirgin kasa 500 daga kamfanin Siemens. Wannan kwangilar zata ci kudi sama da Euro miliyan 300. Hakazalika kasashen biyu sun amince su kara ba juna hadin kai a fasahohin samar da makamashi na zamani.