1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANC ta yi watsi da batun tsige Jacob Zuma

Gazali Abdou Tasawa
November 29, 2016

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya ketara siradin yunkurin da wasu shika-shikan jam'iyyarsa ta ANC suka yi na neman tilasta masa sauka daga kan mulki a bisa zargin cin hanci da karbar rashawa. 

https://p.dw.com/p/2TTJb
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya ketara siradin yunkurin da wasu shika-shikan jam'iyyarsa ta ANC suka yi na neman tilasta masa sauka daga kan mulki a bisa zargin cin hanci da karbar rashawa. Bayan wani zaman tattaunawa na kwanaki uku da shugabannin jam'iyyar ta ANC suka yi kan wannan batu, daga karshe sun yanke shawarar kin bada goyon bayansu ga yunkurin neman tilasta wa Shugaba Zuman wanda wa'adin mulkinsa ke kawo karshe a shekara ta 2019 sauka daga kujerar mulki.

Wasu ministoci uku na gwamnatin ta shugaba Zuma ne suka bukaci da ya yi murabus domin bai wa jam'iyyar damar tsira da dan sauran mutuncinta a idon 'yan kasar dama duniya, bayan da aka bankado badakalar facaka da kudin kasa da ake zarginsa da aikatawa, lamarin da ya soma yin illa ga makomar jam'iyyar ta ANC wacce ta sha dan karen kayi a zaben kananan hukumomi na watan Agustan da ya gabata.