1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaton Kabila ne zai lashe zaɓen Kwango.

November 14, 2006
https://p.dw.com/p/BucA

Bisa dukkan alamu dai, shugaban ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango mai ci yanzu, Joseph Kabila ne ake hasashen cewa zai lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar, bayan an kusan kammala ƙirga duk ƙuri’un. Ƙiyasin da aka yi kawo yanzu na nuna cewa, Kabilan ne ke kan gaban abokin hamayyarsa Jean-Pierre Bemba. Zaɓen Kwangon dai shi ne na farko a ƙasar tun rikicin da aka shafe shekaru 5 ana yi.

A halin yanzu dai, rahotanni sun ce ana samun hauhawar tsamari a babban birnin ƙasar wato Kinshasa, sakamakon wani ɗauki ba daɗin da magoya bayan abokan hamayyar suka yi da juna a ƙarshen makon da ya gabata. ’Yan sandan ƙasar sun ce sun kame fiye4 da mutane ɗari 3, mafi yawansu, marasa galihu, a cikinsu har da yara da dama, waɗanda suka ce su ne ’ummal aba’isin ɓarkewar rikice-rikicen.