Ana zargin kamfanin Daimler Benz da Cin Hanci | Siyasa | DW | 24.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana zargin kamfanin Daimler Benz da Cin Hanci

Mahukuntan Amirka na zargin kamfanin Daimler Benz da laifuka na cin hanci a sakamakon haka aka gurfanar da shi gaban kotun don cinsa tarar kuɗi

default

Babban Motar Daimler

Kamfanin ƙera motocin Marsandi na Daimler, mallakar Jamus, ya amince biyan hukumomin Amirka kuɗi dala miliyan 185, domin cimma sulhu - a wajen kotu, bisa zargin da ita Amirka ke yiwa kamfanin na bayar da cin hanci ga jami'an wasu ƙasashen duniya - a ƙoƙarin samun manyan kwangilolin sayan motoci a ƙasashen.

Masu gabatar da ƙara a ƙasar Amirka dai, sun zargi kamfanin Daimler da bayar da cin hanci na miliyoyin dala ne ta hanyar miƙa kuɗi zunzurutu, ko kyaututtuka, da ɗaukar nauyin kuɗaɗen da jami'an gwamnatoci ke kashewa a lokacin hutu, kana da bayar da manyan motoci - ƙirar marsandi ga jami'ai domin samun kwangila a kimanin ƙasashe 22.

Wata majiyar data buƙaci a sakaya sunanta, ta ce, cimma yarjejeniya a wajen kotun, zata kawo ƙarshen taƙaddamar shari'ar dake tsakanin masu shigar da ƙara akan manyan laifuka da kuma masu tabbatar da bin dokoki na Amirka a ɓangare guda, da kuma shugabannin kamfanin Daimler a ɗaya ɓangaren.

Majiyar ta ƙara da cewar, ko da shike ya zuwa yanzu ba'a kaiga ƙulla wannan yarjejeniyar - a hukumance ba, amma a ranar 1 ga watan Afrilu ne Alƙali zai yanke hukunci akan batun. Sai dai kuma, kakakin kamfanin dama na ma'aikatar kula da harkokin shari'a ta Amirka sunƙi cewa komi game da wannan bayanin.

A baya dai, kamfanin na Daimler, ya amsa cewar, akwai wasu kuɗaɗen da aka bayar - ba bisa ƙa'idah ba a wasu ƙasashe, kana akwai musayar bayanai a tsakanin kamfanin da kuma masu gabatar da ƙara na Amirka da Jamus.

Wani rahoton shekara-shekara da kamfanin ya fitar a shekara ta 2009, ya nuna cewar, Daimler ya ɗauki matakai daban-daban da nufin kawo ƙarshe, da kuma warware batutuwan da masu binciken suka gano, kana da hana afkuwar wani abinda bai dace ba a nan gaba.

Ƙa'rar da hukumomin Amirka suka shigar a gaban wata kotun dake birnin Washington dai, ta zargi Daimler - kamfanin ƙera motocin marsandi da kuma manyar motocin treller a duniya, da laifin rungumar ɗabi'ar bayar da cin hanci ga jami'an ƙetare na tsawon shekaru da dama, domin samun kwangiloli daga gwamnatocin da yake yin hulɗar cinikayya da su.

Zarge-zargen dai, sun haɗar da bayar da fiye da kuɗi Euro miliyan ukku, kwatankwacin dalar Amirkla miliyan 4 - a matsayin cin hanci ga jami'an gwamnatin Rasha da nufin samun kwangilar sayan motoci na Euro miliyan 64 da miliyan 600. Sai kuma kashe fiye da Euro miliyan 4 domin ɗaukar nauyin hutu da kuma bayar da kyaututtuka ga jami'an ƙasar China. Kazalika, kamfanin na Daimler ya bayar da cin hanci domin samar da motocin ɗaukar kayayyaki ga hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Iraqi - a ƙarƙashin shirin Majalisar na musayar abinci da man-fetur.

Wasu daga cin hancin kuma, kamfanin ya bayar da sune ta hanyar kamfanin Shell, wanda tushensa ke ƙasar Amirka.

Daga cikin ƙasashen da wannan badaƙalar ta afku dai - harda ƙasashen Nijeriya, Masar, Indonisia, Code Vore da Latvia da China da kuma Rasha. Sauran sune: Crotia, Serbia da Montenegro, Thailand, Turkiyya, Turkmenistan, da Uzbekistan, da Vietnam. Sai kuma ƙasashen Girka da kuma Hungary.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal