Ana zargin CIA da take hakkokin bil adama | Zamantakewa | DW | 25.11.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ana zargin CIA da take hakkokin bil adama

Za a iya gano gaskiyar hakan ta hanyar amfani da tauraron dan adam a cewar wani dan majalisa daga kasar Swiss

Rahotanni dai ya zuwa yanzu na nuni da cewa ba a da bayan wannan zargi na hukumomin kare hakkin bil adama, Jaridar washinton Post ta taba buga wani labari a cikin wannan wata da muke ciki cewa hukumar lekewn asiri ta Amurka ,wato CIA na ganawa wasu yan Alqaeda azaba a wani gidan yari dake boye a gabashin nahiyar Turai.

Ita kuwa hukumar kare hakkokin bil adama ta Human Rights watch cewa tayi da alama kasar Romania da kuma kasar Poland dake daya daga cikin yayan Eu na daga cikin kasashen da hukumar ta CIA ke amfani dasu wajen gudanar da gidajen yarin boye da takan azabtar da fursunoni.

Ya zuwa yanzu dai tuni wadannan kasashe biyu suka fito fili karara suka karyata wannan zargi da cewa bashi da tushe balle makama.

A waje daya kuma jami´in dake kula da kare hakkokin bil adama na kungiyyar ta EU, wato Alvaro Gil Robles ya nunar da cewa akwai wani guri da sojojin Amurka ke amfani dashi a kasar Kosovo a matsayin wani gidan yari na boye to sai dai yace bashi da cikakken bayanin irin alakar dake akwai a tsakanin hakan da hukumar ta CIA ba.

Jaridar Le Monde ta kasa Faransa ta taba rawaito Mr Alvaro na fadin cewa ya girgiza a lokacin da ya gano wannan wuri da sojojin na Amurka ke amfani dashi wajen azabtar da fursunoni a kasar ta Kosovo a shekara ta 2002 data gabata.

A karshe Jaridar ta Le Monde tayi kokarin kwatanta yanayi da fursunonin ke ciki a kasar Kosovo da yanayi da fursunoni ke ciki a gidan yari na Guantanamo Bay dake Cuba, da cewa da yawa daga cikin su na tsare ne ba tare da an gurfanar dasu a gaban kuliya.

Game kuwa da wadannan korafe korafe,tuni majalisar kungiyyar tarayyar Turai ta kaddamar da bincike a kansu, to amma ya zuwa yanzu a cewar majalisar ta Eu jaridar ta Washinton Post taki ta gasgata labarin data buga ko kuma ta karyata.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa a ranar litinin din data gabata ne yayan kungiyyar na Eu suka amince da rubutawa Amurka takarda na neman cikakken bayani game da wannan zargi da ake musu.

A yayin da kuwa ake wannan takaddama,wani dan majalisa daka kasar Swiss cewa yayi idan akayi amfani da tauraron dan adam wato Stellite a turance za a iya gano ko shin hukumar ta CIA nada gidajen yarin boye ko kuma aa.

Mr Dick Marty, wanda ke shirye shiryen gabatar da cikakken rahoto ga majalisar kungiyyar ta Eu a game da wannan shawara daya gabatar, yace tuni ya fara tuntubar zangon tauraron dan adam din dake kasar Spain.

Jami´in yaci gaba da cewa da taimakon wannan na´ura za a iya samun cikakkun hotuna na irin abubuwan dake faruwa daga farkon shekara ta 2002 izuwa yanzu, wanda hakan ka iya bayar da damar sanin ainihin gaskiya ko akasin ta game da wannan zargi da ake.

 • Kwanan wata 25.11.2005
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUE
 • Kwanan wata 25.11.2005
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUE