Ana zaben sabon shugaban kasar Sabiya | Labarai | DW | 02.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana zaben sabon shugaban kasar Sabiya

A bisa kiyasi dan kasar Sabiya tsaka-tsaki na iya samun Euro 330 ne kawai a wata, yayin da ake da kashi 15 cikin dari na marasa aikin yi.

Serbien Präsidentschaftswahl Alexandar Vucic (picture-alliance/dpa/Sputnik/A. Vitvitsky)

Alexandar Vucic dan takarar shugaban kasa a Sabiya

An fara kada kuri'a domin  zaben sabon shugaban kasar Sabiya a wannan rana ta Lahadi, zaben da ake ganin Firaminista Aleksandar Vucic mai karfin fada aji zai kai labari da samun kashi hamshin cikin dari na kuri'un da aka kada tun a zagayen farko.Vucic mai shekaru 47 shi ne dan takarar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a a kasar ta nunar da cewa shi ke gaba, ya dai taka rawa wajen ganin tattalin arzikin kasar ya farfado tun bayan da aka zabe shi firaminista a 2014. Sai dai a bisa kiyasin dan kasar Sabiya tsaka-tsaki na iya samun Euro 330 ne kawai a wata, yayin da ake da kashi 15 cikin dari na marasa aikin yi. Wasu dai na kallon dantakarar a matsayin dan kama karya, ga shi kuma 'yan adawa na Democrats Sasa Jankovic da  Vuk Jeremic kansu ba a hade ba.

Ana dai kallon Vucic a matsayin wanda ya mamaye kafafan yada labarai abin da ake ganin ya taimaka wajen haskakawarsa yayin da sauran 'yan takara basu da dama irin tasa.