Ana tababa kan sahihancin takarar Mr Musharraf | Labarai | DW | 07.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana tababa kan sahihancin takarar Mr Musharraf

Hukumar zaben kasar Pakistan tace dole ne sai shugaba Musharraf ya samu yardar kotun kolin kasar dangane da takarar sa, zai tabbata mutumin daya lashe zaben shugaban kasar. Hakan yazo ne a yayin da ake ci gaba da tababar sahihancin tsayawar Mr Musharraf a zaben shugaban kasar ne . Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Mr Musharraf ya samu kuri´´u 252 daga cikin kuri´u 257 da aka kada ne,a majalisun dokokin kasar.Tuni dai masu nazarin siyasa na kasar suka tsammaci nasarar ta Mr Musharraf a zaben na jiya, duk kuwa da kaurace masa da wasu jam´iyyu na kasar suka yi. A yanzu haka dai manya manyan alkalai na nazarin kundin tsarin mulkin kasar, don tantance sahihancin takarar ta Mr Musharraf, a yayin da yake ci gaba da rike mukamin babban kwamandan sojin kasar. Mr Pavez Musharraf dai yayi alkawarin barin wannan mukamin ne da zarar ya sami nasarar wannan zabe, don ci gaba da mulki a matsayin farar hula,bayan shafe shekaru 8 yana jagorancin kasar a matsayin mulkin soji.