1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANA TA KARA SAMUN HABAKAR TASHE-TASHEN HANKULLA A IRAQI.

YAHAYA AHMEDApril 8, 2004

Shekara daya ke nan da dakarun Amirka suka kame babban birnin kasar Iraqi Bagadaza, abin da kuma ke alamta tumbuke gwamnatin Saddam Hussein. Amma har ila yau, ba a sami sassaucin tsamari a kasar ba. Wai shin, rikicin baya-bayan nan da ya barke a kasar, tarzoma ce kawai, ko kuwa wani sabon yaki ne ya kunno kai a Iraqin ?

https://p.dw.com/p/Bvks
Sojojin Amirka, kusa da wani masallaci a Falluja, a fafatawar da suke yi da `yan tawayen Iraqi
Sojojin Amirka, kusa da wani masallaci a Falluja, a fafatawar da suke yi da `yan tawayen IraqiHoto: AP

A ran 9 ga watan Ifirilun shekarar bara ne, sojojin Amirka suka hambarad da wani gundumemen mutum-mutmin Saddam Hussein da ke kafe a babban dandalin birnin Bagadaza. Ko awa daya ba a yi ba, sai kusan duk tashoshin talabijin na duniya suka dinga nuna hoton mutum-mutmin da ke kwance a kasa, abin da ke alamta kawo karshen mulkin Saddam Hussein a kasar Iraqi. A hotunan dai ana iya ganin wani soja yana tsaye kan mutum-mutumin dauke da tutar Amirka. Ga al’umman Iraqin dai, wannan na nuna alamun manufar Amirkan ne a kasar, wato ta cusa musu nata ra’ayoyi da kuma kafa ikonta a kasar. Duk da cewa, da yawa daga cikinsu, ba sa goyon bayan Saddam Hussein, sun dauki dora tutar Amirka kan mutum-mutumin da sojojin Amirkan suka yi ne, tamkar wani wulakanci gare su.

Tun wannan lokacin ne kuma, a daura da zaton da dakarun mamayen suka yi, na cewa, za su kasance su ne masu fada a ji a Bagadaza, sai aka wayi gari `yan kasar Iraqin na nuna musu matukar adawa, inda rukunan `yan bindiga daban-daban ke ta kai musu hare-hare. A cikin shekara daya da ta wuce dai, masu adawar sun yi ta kara samun gyoyon bayan jama’ar Iraqin.

Rikice-rikce kuma, sai kara habaka suka yi ta yi. Rikicin baya-bayan nan da ya barke, wanda kuma ya fi tsanani, shi ne karawar da magoya bayan shugaba darikar shi’itin nan Moqtada as-Sadr suka yi ta yi da sojojin mamaye a yankuna daban-daban na kasar. Har ila yau dai ana ci gaba da wannan arangamar, kuma a kullum, rahotanni na nuna cewa, lamarin sai kara tabarbarewa yake yi.

Wasu masharhanta ma na ganin cewa, wani sabon yaki ne ya barke a Iraqin, inda a halin yanzu, dakarun mamayen ba sa iya bambanta masu yakansu da sauran fararen hulan kasar. A ko’ina, ko a birane ne, ko a yankunan karkara, babu abin da ake ji sai hargagin bindigogi da na tashin bamabamai. Rahotanni dai na nuna cewa, rukunan dakarun mamayen sun fara kai hare-haren bamabamai kan wasu masssalattai, inda jama’a suka taru don yin ibada ko kuma suka nemi mafaka.

A halin yanzu dai, za a iya cewa, Washington na cikin wani hali ne na rudami. Ba ta san yadda za ta shawo kan matsalar, a Iraqin da kuma a wasu wurare ba, kamar dai a rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

Sakataren tsaron Amirka Rumsfeld da wasu manyan kusoshin gwamnatin shugaba Bush, na bayyana ra’ayin cewa, mai da martani da daukan matakan soji ne kawai abin da zai magance matsalar. Tuni dai, Amirkan ta fara tura karin yawan dakaru zuwa Iraqin, maimakon ta rage yawansu. Wani rukunin sojinta kuma ya sami umarnin ya farauto shugaban shi’itin nan Moqtada as-Sadr.

Babu shakka, a halin da ake ciki yanzu dai, shugaba Bush ba zai iya janye sojojinsa hakan nan daga Iraqin ba. Yin hakan, zai tabbatar masa da shan kaye ne a zaben shugaban kasar Amirka da za a yi a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Bugu da kari kuma, Iraqin za ta fada cikin wani mummunan hali ne, da ba za a iya yin kiyasin sakamakon da hakan zai haifar ba a halin yanzu.

`Yan kasar Iraqin dai, ba su cancanci fadawa cikin wani mummunan hali ba kuma. Bayan kasancewa karkashin mulkin danniyar Saddam Hussein a shekaru da dama, yanzu kamata ya yi, a ce sun sami damar kafa gwamnatin hadin kan kasar cikin adalci da kuma zaman lumana.

Amma ko me Amirka ta yi kuma, da wuya ta sami goyon bayan jama’ar kasar, saboda kwarjininta ya dusashe a yankin baki daya. A ko’ina dai, shakku ake nunawa ga manufofinta. Abin da zai cece ta kawai shi ne ta mika ragamar tafiyad da harkokin Iraqin ga Majalisar dinkin Duniya. Sai dai, ba lalle ba ne Majalisar ta amince ta dawowa Iraqin hakan nan, ba da shimfida wasu sharudda ba, tun da ita ma, `yan adawar Iraqin ba barinta suka yi ba. Su ne ma suka tilasa mata janye mafi yawan jami’anta daga birnin Bagadaza.