Ana ta kara samun habakar gibin tattalin arziki tsakanin kasashe mawadata da masu tasowa. | Zamantakewa | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ana ta kara samun habakar gibin tattalin arziki tsakanin kasashe mawadata da masu tasowa.

Minstan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta gana da shugaban Hukumar kula da Ayyukan ba da Taimakon Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, wato UNDP a takaice, Kemal Dervis, a ofishinta a birnin Berlin.

Heidemarie Wieczorek-Zeul, ministan ayyukan ba da taimamon raya kasashe ta tarayyar Jamus.

Heidemarie Wieczorek-Zeul, ministan ayyukan ba da taimamon raya kasashe ta tarayyar Jamus.

Ministan ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta ce manufar ba da taimakon raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, na daya daga cikin jigogin manufofin da gwamnatinta ta sanya a gaba. Sabili da haka ne kuwa take goyon bayan shirin yi wa hukumar UNDP din kwaskwarima. Ministan ta bayyana hakan ne bayan wata ganawar da ta yi a ofishinta a birnin Berlin, da shugaban Hukumar Kula da ayyukan ba da taimamon raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, wato UNDP a takaice, Kemal Dervis. Ta ce matsayin gwamnatin tarayyar a kan wannan batun shi ne:-

„Muna goyon bayan garambawul da ake niyyar gudanarwa a hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, batun da ya kasance jigon tattaunawar da aka yi ta yi a shekarar bara. An dai shirya kafa wani kwamiti wanda zai dinga kulawa da bunkasa ayyukan zaman lafiya, wato Peace Building Commission a turance, da kuma kafa kwamitin mashawarta kan batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam. Wannan kwamitin dai zai kasance mai zaman kansa ne. Kuma zai dinga sa ido ne kan take hakkin dan Adam a duniya, ya kuma dau matakan da suka dace don hana yaduwar wannan illar.“

Ministan dai ta ce a shawarwarin da ta yi da shugaban hukumar na UNDP, sun kuma tattauna batun shirin nan da aka yi wa lakabi na karni, wanda ya tanadi inganta halin rayuwar al’umman kasashe masu tasowa, musamman ma dai a fannin yakan talauci. A nan dai, inji ministan, ba a sami nasarar da aka yi hasashensa ba. Amma ta kara da cewa:-

„Yana da muhimmanci dai a bayyana irin nasarar da aka samu; wato tsakanin 1990 zuwa shekara ta 2002, an sami ragowar yawan masu huskantar matukar talauci a duniya da mutane miliyan dari da 30, kazalika kuma mutane biliyan 1 da ddigo 2 ne suka sami hanyar samun ruwan sha mai tsabta da kuma ingantattun kafofin kiwon lafiya. Sai dai, yunkurin cim ma burin shirin na karni kafin shekara ta 2015, musamman dai a nahiyar Afirka, na bukatar mu duka, mu zage dantse, mu yi hobbasa, kafin mu sami nasara.“

Kemal Dervis, wanda ya ke rike da shugabancin Hukumar Kula da ayyukan ba da taimakon raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniyar tun watan Agusta na shekarar bara, ya bayyana cewa da akwai ayyuka da yawa nan gaba, kafin a iya cim ma burin shirin wannan karnin, duk da cewa, miliyoyin jama’a sun kubuta daga kangin talauci a kasashe kamarsu Indiya da Sin a cikin `yan shekarun baya da suka wuce. Ya kara bayyana cewa:-

„Idan aka dubi yadda all’amura suke a halin yanzu dai, sai a ga cewa har ila yau tafiyar hawainiya ake yi. Kashi 80 cikin dari na al’umman duniya dai na cikin wani hali ne inda gibi tsakanin mawadata da marasa galihu ke ta kara habaka maimakon ya ragu.“

Jami’in dai ya kara bayyana cewa, muddin ba a kara ba da taimako ba, to cim ma burin da aka sanya a gaba zai yi wuya a lokaci mai tsawo. daya fannin da akka fi huskantar matsala ne fannin kiwon lafiya.

Ministan ta Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul ta tabbatar wa jaim’in cewa, gwmantinta na duk iayakacin kokarinta wajen ganin cewa ta cika alkawarin da ta dauka na ba da karin kudi na kashi sifili da 33 cikin dari na kudaden shigarta ga asusun ba da taimakon raya kasashe.