1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ta ci gaba da zanga-zangar nuna adawa ga zanen izgina wa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a Kasashen musulmi.

February 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv98

A cikin zanga-zangar da ake ta yi a duniyar musulmi, dangane da batancin da aka yi wa annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a jaridun wasu Kasashe na Yamma, rahotanni sun ce mujtane 4 sun rasa rayukansu a Kasar Afghanistan, yayin da dimbin yawan masu zanga-zanga suka kara da jami’an tsaro a gabashin Kasar. Jami’an gwamnatin jihar da tarzomar ta auku, sun ce `yan sanda sun bude wa masu zanga-zangar wuta ne, bayan da suka fara jifansu da duwatsu. A halin da ake ciki dai, shugabannin duniya na ci gaba da kira ga kwanciyar hankali. Gwamnatin tarayar Jamus ta shawarci babban sakataren Majalisar dinkin Duniya Kofi Annan, da ya kira wani taro na addinan duniya don tattauna batun inganta zaman cude ni in cude ka da juna.

A wata sabuwa kuma, ministan harkokin wajen Denmark Per Stig Möller, ya fara neman yin shawarwari da Kungiyar Musulmi ta Duniya, wadda ke wakilcin Kasashen musulmi 57. Kungiyar dai ta bayyana cewa, hare-haren da aka kai kan ofisoshin jakadancin Kasashen Denmark da Norway a biranen Beirut da Damascus, wato wuce gona ne da iri.