1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana ta ƙara samun tashe-tashen hankulla a Iraqi

Har ila yau dai, an gaza cim ma kwanciyar hankali a ƙasar Iraqi. Tun ran lahadi da ta wuce ne wani shirin da Firamiyan ƙasar, Nuri al-Maliki ya gabatar, ya fara aiki, da burin kwantad da ƙurar rikice-rikicen da ake ta yi. Amma kwana ɗaya tak bayan gabatad da wannan shirin, sai ga shi ana ci gaba da kai hare-haren bamabamai a yankuna daban-daban na ƙasar.

Firamiyan Iraqi, Nuri al-Maliki, lokacin da yake gabatad da shirinsa na sulhu.

Firamiyan Iraqi, Nuri al-Maliki, lokacin da yake gabatad da shirinsa na sulhu.

Alƙaluman da aka buga, kan asarar rayukan da hare-haren baya-bayan nan suka janyo a Iraqi, sun bambanta. Kamfanonin dillancin labaran kasashen Yamma sun ce, a ƙalla rayuka 15 ne suka salwanta a hare-haren da aka kai a garin Hilla da ke kudancin birnin Bagadaza. Amma wakilan gidajen talabijin na ƙasashen Larabawa a ƙasar sun ce kusan mutane 30 ne suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 50 kuma suka ji rauni.

Wata sanarwar da ’yan sanda suka bayar game da harin dai, ta ce bam ne ya tashi a kasuwar garin na Hilla, a daidai lokacin da ake cinkoson jama’a da yamma kafin kasuwar ta tashi. Bayan tashin bam ɗin ne kuma jama’a suka afka wa ’yan sanda, suna jifansu da duwatsu, don nuna fusatarsu ga gazawar jami’an tsaron, wajen hana aukuwar hare-haren.

Sau da yawa, tun da aka hamɓare Saddam Hussein, ’yan tawaye sun sha kai hare-hare a garin na Hilla. Wani mummunan harin da suka kai a garin a cikin watan Fabrairun da ya gabata, ya janyo asarar rayukan mutane 118. ’Yan ƙungiyar al-Qaeda a Iraqin, ƙarƙashin jagorancin Abu Musab al-Zarqawi, wanda dakarun Amirka suka kashe a wani ɗauki a farkon wannan watan, sun yi ikirarin kai hare-haren.

A halin yanzu dai, ’yan ƙungiyar al-Qaedan ne aka keɓe daga cin moriyar wani shirin afuwa da gwamnatin Iraqin ta gabatar. A cikin shirin, wanda Firamiya Nuri al-Maliki ya gabatar a ran lahadin da ta wuce, an tanadi gudanad da shawarwarin sulhu tsakanin gwamnatin da sauran ƙungiyoyin ’yan tawayen da ba su da wata jiɓinta da al-Qaeda ko kuma masu nuna biyayya ga tsohon shugaba Saddam Hussein. A nan dai, wato ana nufin ’yan yakin gwagwarmaya ne na ɗariƙar Sunni, waɗanda suke yaƙan dakarun mamaye na ƙetare a ƙasar.

Bisa wani rahoton da da jaridar nan ta “Al-Sabah“ ta buga dai, ƙungiyoyin ’yan ɗariƙar Sunnin guda 7 ne ake sa ran za su amince da shirin. Amma harin da aka kai jiya a garin Hilla na musanta wannan zaton da ake yi. Masharhanta na ganin harin ne tamkar, sanya wata alama ta nuna adawa ga shirin na Firamiya al-Maliki. A cikin ’yan kwanakin da suka wuce dai, kusan mutane 40, dukkansu ’yan ƙasar Iraqin ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankullan da suka auku a ƙasar. Ma’aikatar harkokin cikin gidan Iraqin, ta ce a birnin Bagadaza, wani ɗan harin ƙunan baƙin wake ya ta da bam, inda ya ritsa da ’yan sanda biyu. Kazalika kuma, sojojin Iraqin 5 ne suka sheƙa lahira, sakamakon ta da bam da aka yi cikin mota a birnin na Bagadaza. Har ila yau dai, a wani ɗauki ba daɗin da dakarun Amirka suka yi da ’yan tawaye a jihar El Anbar da ke yammacin ƙasar, wani sojan Amirkay a mutu, sakamakon raunin da ya ji a fafatawar.

 • Kwanan wata 27.06.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzc
 • Kwanan wata 27.06.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzc