Ana ta ƙara samun hauhawar tsamari a yankunan Falasɗinawa. | Labarai | DW | 15.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ta ƙara samun hauhawar tsamari a yankunan Falasɗinawa.

Rikice-rikice tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa masu hamayya da juna a Zirin Gaza, sun fara yaɗuwa zuwa Gaɓar Yamma, inda rahotannin da muka samu ke nuna cewa an yi wata ƙazamar musayar wuta tsakanin magoya bayan ƙungiyar Hamas da na Fatah a yankin, abin da ya janyo mutuwar wani mutum ɗaya. Kafin hakan dai, an girke dubban jami’an tsaron ƙungiyar Hamas a Zirin Gaza, sakamakon abin da ƙungiyar ke gani kamar wani yunƙurin da aka yi, na yi wa Firamiyan Falasɗinawan Ismail Haniya, kisan gilla, yayin da aka buɗe wa ayarin motocinsa wuta jiya a kan iyakar Gazan da Masar. Ita Hamas ɗin dai na zargin jami’an tsaron iyakar Falasɗinawan na ƙungiyar Fatah ne da buɗe wa motar Firamiyan wuta. A musayar wutar da ta auku a kan iyakar dai, rahotanni sun ce an kashe ɗaya daga cikin masu kare lafiyar Firamiyan, sa’annan ɗaya daga cikin ’ya’yansa kuma ya ji rauni. Wasu rahotanni kuma sun ce dakarun Isra’ila, sun hana Firamiyan Falasɗinawan shigowa da kuɗi kimanin dola miliyan 35 zuwa Zirin Gazan. A halin da ake ciki dai, shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas, ya musanta zargin da ƙungiyar Hamas ke yi wa jami’an tsaron iyakar na ƙungiyarsa ta Fatah, na cewa su ne suka fara buɗe wuta. Ya kuma yi kira ga shugabannin addini da su gargaɗi jama’a da su guji shiga duk wasu ayyukan tashe-tashen hankulla, a huɗubarsu ta salar juma’a yau.