Ana ta ƙara gano gawawwakin waɗanda annobar ta Tsunami ta ritsa da su a Indonesiya. | Labarai | DW | 19.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ta ƙara gano gawawwakin waɗanda annobar ta Tsunami ta ritsa da su a Indonesiya.

Jami’an ƙasar Indonesiya, sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon tashin igiyar ruwan nan ta tsunami a kan tsibirin Java a ran litinin da ta wuce, ya tashi zuwa sama da ɗari 4. Wata girgizar ƙasa a ƙarƙashin teku, mai ƙarfin awo 7 da ɗigo 7 a kan mizanin Richter ne ta janyo annobar. Igiyar ruwar, wadda ta kai tsawon mita 2 ta ragargaz duk wasu matsugunai da ke gaɓar tekun tsakiyar tsibirin na Java.

Gwamnatin Indonesiyan dai ta ce har ila yau, ba ta da isassu, kuma ingantattun na’urori, don gano ɓarkewar irin wannan annobar a cikin lokaci.