1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ta ƙara samun hare-haren bamabamai a ƙasar Iraqi.

May 31, 2006
https://p.dw.com/p/Buw0

Rahotannin da ke iso mana daga Iraqi, sun ce a ƙalla mutane 46 ne suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 100 kuma suka ji rauni, a ci gaba da hare-haren bamabamai da ake ta kaiwa a faɗin ƙasar. Wani bam da ya tashi a gabashin birnin Bagadaza, ya halaka mutane 25, tare da ji wa fararen hula 65 raunuka. Har ila yau dai, a birnin na Bagadaza, rahotannin sun ce wani sojan Amirka ya gamu da ajalinsa, yayin da wani bam da aka dasa a gefen titi ya tashi jiya daddare a kudu maso gabashin birnin. Kawo yanzu dai, yawan sojojin Amirka da aka kashe a Iraqin tun da afka mata da yaƙi da aka yi a shekara ta 2003, ya kai dubu 2 da ɗari 4 da 71, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito, bisa alƙaluman ma’aikatar tsaron Amirkan, wato Pentagon.

A wata sabuwa kuma, ministan harkokin wajen ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, ya ba da sanarwar cewa an cim ma sako wani jami’in diplomasiyyan ƙasar, Naji Al Nu’aimi, wanda aka yi garkuwa da shi a Iraqin tun ran 16 ga wannan watan.