Ana shirin yin tattaunawa tsakanin Ahmedinejad da sarki Abdullah na Saudiya
March 3, 2007Talla
Shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ya ce zai yi amfani da ziyararsa ta biyu a Saudiya don tattaunawa akan yadda Iran da daular ta Saudiya zasu iya aiki tare don rage hauhawar tsamari a yankin GTT. Shugaba Ahmedi Nijad ya fadawa manema labarai a filin jirgin saman birnin Teheran kafin ya tashi zuwa birnin Riyadh cewa zai tattauna da sarki Abdullah akan hadin kan da za´a bawa juna a cikin duniyar musulmi da kuma yankin GTT. Shugaban na Iran wanda Amirka ke zargin kasarsa da dagula lamura a yankin, ya ce a shirye Iran ta ke ta yi duk iya kokarin ta don rage rigingimun siyasa a Lebanon. A yau dai ne Ahmedi Nijad ke fara ziyarar aiki ta yini biyu a Saudiyya, wadda take zama babbar kawar Amirka.