Ana sayar gine-ginen coci ana mayar da su masallatai | Zamantakewa | DW | 03.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ana sayar gine-ginen coci ana mayar da su masallatai

Ƙarancin masu ibada a majami´un ya sa ake sayar da wuraren ibadar na Kiristoci

default

Cocin St. Petri a Saxony-Anhalt

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Ana mayar da coci-coci zuwa masallatai wannan dai shi ne kanun labarun da ya fi ɗaukar hankalin manyan kafofin yaɗa labaru a Jamus a cikin makonnin baya bayan nan. Kamar manyan majami´un addinin Kirista wato kamar Katholika da Evangelika su ma ƙananan majami´u irin su New Apostolic su ma suna fuskantar matsalar ƙarancin mabiya ɗarikunsu. Hakan kuwa na haifar da wani mummunan sakamako inda wuraren ibadarsu wato kamar coci ke kasancewa wayam babu isassun masu ibada dake zuwa. Bisa wannan dalili ne yanzu shugabannin coci coci suka yanke shawarar sayar da wuraren ibadarsu ga masu sha´awar saya. Yanzu haka ma dai a birnin Berlin hedkwatar gwamnatin tarayyar Jamus, an yi tallar wasu gidajen ibadar na coci coci guda biyu ta yanar gizo wato intanet, kuma tuni har wasu kungiyoyin musulmi larabawa sun sayesu. A lokacin da jaridu da sauran kafofin yaɗa labaru suka buga labarin sayar da coci ga ƙungiyoyin musulmin, an yi mayar da martani iri daban daban musamman ganin yadda ba a daɗe ba da tabka wata zazzafar muhawwara a dangane gina masallatai a nan Jamus.

Wannan dai a wani masallaci ne inda musulmi maza kimanin 50 suka taru suna salla. Masallacin dai a cikin wani gini ne inda a da ya ƙunshi wani cocin darikar New Apostolic dake unguwar Neukölln a birnin Berlin. A wani ɗaki dake saman kuma an warewa mata ne musulmi. Ko da yake mutanen da suka hallara a masallacin suna da fara´a kuma suna nuna girmamawa ga baki, amma sun ki a dauki muryoyinsu a rikoda. Maimakon haka sun nemi duk mai son karin bayani da ya tuntubi wata kungiyar hadin kan al´adu wadda ta saye ginin akan kuɗi euro dubu 550. To sai dai kungiyar ba sananniya ba ce ga jama´a.

A hirar da aka yi da shi ta wayar tarho shugaban ta Mohammed Taha ya yi nuni da cewa burinsu shi ne su mayar da tsohon ginin cocin wani wuri da za a yi amfani da shi a ɓangarori da dama. Ya ce a yanzu za su ci-gaba da amfani da shi a matsayin masallaci to amma a ƙarshe aikin ibadar zai kunshi kashi 10 ne cikin 100 na ayyukan da za a yi a cikin ginin. Ya ce za a fi mayar da hankali a aikace aikace kamar faɗakarwa dangane da kyautata zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka ba da shawarwari kan zamantakewa, kwasa-kwasai na sana´o´i da kuma aikin tafinta musamman ga baki.

Su ma wakilan ƙungiyar Al Torath ta al´umar musulumi ´yan asalin ƙasar Iraqi ta na da irin wannan ra´ayi. Ƙungiyar ta Al Torath ita ta saye ɗaya ginin coci na ɗarikar New Apostolic dake unguwar Tempelhof a kan farashi mai tsada a birnin Berlin. Mohammed ma´ajin ƙungiyar ya jaddada cewa ba su da niyar mayar da ginin masallaci, sannan sai ya ƙara da cewa.

“A nan masallacin ba ma gudanar da addu´o´i na addini, in ban da bukukuwa na addini da wasu tarurruka da suka shafi addini. Nan gaba kaɗan za mu fara koyar da ilimin addini musamman ga yara ƙanana, wato musulmi da waɗanda ba musulmi ba waɗanda ke zuwa makarantu dake cikin wannan unguwa. Bugu da ƙari za mu kuma fara koyar da harshen Jamusanci ga waɗanda ba Jamusawa ba, sannan su kuma Jamusawa za mu fara koyar da su Larbaci.”

Ƙungiyar ta Al-Torath ana alaƙanta ta ga limamin limaman ´yan ɗarikar Shi´a mai sassaucin ra´ayi a Iraqi, Ayatollah Ali al-Sistani. Daga cikin membobi masu rajista a kungiyar su kimanin 40 akwai Jamusawa waɗanda suka musulunta. Daga cikinsu kuwa akwai wani ɗalibi Bajamushe mai suna Maxmilian Voigt wanda ke karatun harshen larbaci a jami´a. Voigt dai ɗaya daga cikin shugabannin zartaswan kungiyar ta Al-Torath.

“A cikin addinin muusulunci akwai banbanci tsakanin masallaci wanda aka yi masa gini irin na wurin ibadar musulmi da kuma ɗakunan taruwan jama´a waɗanda ake iya yin sallah a cikinsu. Da farkon farawa ana ɗaukar nan wurin da muke magana kansa a matsayin wata cibiyar ta wannan gamaiya maimakon wani masallaci, inda ake a kullum musulmi za su iya zuwa suna sauke farali a ciki. Saboda haka aka bude wannan wuri ga kowa. Ba ma bukatar wata alama ta ginin masallaci wato kamar hasumiya.”

Kyautata zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka na ƙara samun karbuwa tsakanin jama´ar wannan kasa. Dangane da haka kungiyar ta ƙuduri aniyar cimma wannan manufa ta hanyar buɗe kofofinta ga kowa. Watakila saboda muradin samun yarda ya sa shugabannin ƙungiyar suka kasa fitowa fili su bayyana cewa zasu mayar da tsohon ginin coci wata cibiyar ibada ko masallaci. To amma tuni wasu rahotanni na kafofin yaɗa labaru sun yi nuni da haka. Shugabannin cocin New Apostolic Church ba su damu da abin da za a yi da ginin ba kamar yadda shugaban sakatariyar cocin a birnin Berlin Carsten Höhn ya nunar.

“Ga yadda muka fahimci ginin wurin ibada a cikin majami´armu, shi ne gini kamar na coci na rasa matsayinsa musamman na wani wurin ibada ko wani wuri mai tsarki da zarar an daina yin wasu aikace aikace na ibada a cikinsa. A da dai suna da wannan matsayin domin sun kasance wurare ne da ake aikin Allah a ciki. A nan dai ina mai ba da misali da aya ta 18 a sura ta Matthias a littafin Bible wadda ke cewa duk inda mutane biyu ko uku suka taru don yi mini ibada to Zan kasance a tsakaninsu.”

Ya ƙara da cewa ba sa adawa da musulmin da suka saye wurin. Ya ce hana su sayen wurin saboda dalilai na banbancin addini ka iya janyo zarge zarge na nuna wariya. To sai dai ra´ayin darikun Katholika da Evangelika ya banbanta. A cikin shekaru kalilan masu zuwa za su rufe gidajen ibada kimanin dubu 10 a Jamus saboda ƙarancin masu zuwa ibada. Amma waɗannan darikun guda biyu sun ce ba za su sayarwa wasu mabiya addinai da ba na kirista wadannan wurare. Su ka ce sun gwammace su rushe gine-ginen coci ko su bar su haka ba a amfani da su ko kuma su sayarwa ´yan kasuwa. To sai dai mai kula da batutuwan baƙi a unguwar Neokölln dake birnin Berlin na mai ra´ayin cewa dakin Allah ɗakin Allah ne ko coci ko masallaci.