Ana samun sabani game da ranar da za´a rataye Saddam Hussein | Labarai | DW | 29.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana samun sabani game da ranar da za´a rataye Saddam Hussein

Wani jami´in gwamnatin Iraqi ya musanta rahotannin da aka bayar cewa ana iya rataye Saddam Hussein a gobe asabar. To amma lauyoyin tsohon shugaban na Iraqi sun ce yana shirin a aiwatar da hukuncin kisan akan shi. A daidai lokacin da ake yada jita-jita game da lokacin zartas da hukuncin kisan, ma´aikatar shari´a ta Iraqi ta musanta bayanan da lauyoyin dake kare tsohon dan mulkin kama karyan suka yi cewa rundunar sojin Amirka ta mika shi ga hukumomin Iraqi. Babban jimi´in ma´aikatar shari´ar ya ce ba za´a zartas da hukuncin kisan ba gabanin ranar 26 ga watan janeru, wato kwanaki 30 bayan an amince da hukuncin da aka yanke masa.