1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana samun nasara a yaki da Maleriya

Mouhamadou Awal BalarabeDecember 9, 2014

Hukumar lafiya ta duniya ta nunar cikin rahotonta na shekara 2014 cewa zazzabin cizon sauro ya ja baya da 47% a cikin shekaru 14 da suka wuce musamman a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1E1Dm
Hoto: Sanaria Inc

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa zazzabin cizon sauro na maleriya ya ja baya a cikin shekaru 14 da suka gabata idan aka yi la'akari da yawan mutane da ta hallaka a duniya. Sai dai kuma ta yi gargadi kan gibin da ake samu na karancin magungunan wannan cuta da kuma gidajen sauro dake dauke da magani.

Cikin rahotonta na shekara shekara da ta wallafa a wannan Talarar, WHO ko kuma OMS ta ce mutane da ke rasa rayukansu sakamakon kamuwa da Maleriya sun ragu da kashi 47 daga cikin 100 tsakanin shekarun 2000 zuwa 2013.

A kasashen Afirka dake Kudu da Sahara inda aka fi fama da zazzabin na cizon sauro, an samu raguwar kashi 54 daga cikin 100 na wadanda cutar ke kashewa. Sai dai kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta nunar da cewar kasashen yammacin Afirka dake fama da annobar Ebola na fuskantar barazanar yaduwar cutar ta maleriya.