1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana samun karuwar fyade ga 'yan Rohingya

Yusuf Bala Nayaya
September 27, 2017

Darakta Janar William Lacy Swing na kungiyar kula da kaurar jama'a ta kasa da kasa IOM ya ce ya kadu matuka sakamakon rahotannin cin zarafi ta hanyar lalata ga mutanen da suka isa Bangaladash.

https://p.dw.com/p/2kpwG
Bangladesch Myanmar Grenze Rohingya Flüchtlinge
Hoto: Reuters/D. Siddiqui

Jagoran kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya ya yi gargadin cewa akwai karuwar rahotanni na aikata fyade ga mata musulmi 'yan kabilar Rohingya wadanda ke gudun tashin hankali a Myanmar a 'yan makonin nan.

Darakta Janar William Lacy Swing na kungiyar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM ya ce ya kadu matuka game da rahotannin cin zarafi ta hanyar lalata ga mutanen da suka isa Bangaladash a baya-bayan nan.

Akwai kimanin mutane 480,000 da suka isa garin Cox's Bazar tun daga ranar 25 ga watan Agusta. Likitoci da ke aiki karkashin kungiyar ta IOM na bada kulawa ta musamman ga mata da suka fuskanci cin zarafi akan hanyarsu a cewar Swing, sai dai ya ce adadin na zama kadan kasancewar ba kowa ke fadin bala'in da ya gani a kan hanyarsa ba.