Ana samun ci-gaba a tattaunawar zaman lafiya a arewacin Uganda | Labarai | DW | 30.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana samun ci-gaba a tattaunawar zaman lafiya a arewacin Uganda

Gwamnati da ´yan tawaye a Uganda sun samu ci-gaba a tattaunawar samar da zaman lafiya da suke yi tsakani. A gun taron da suke yi a kudancin kasar Sudan sassan biyu sun amince da kafa wani kwamiti wanda zai gudanar da bincike akan zargin aikata laifukan yaki da ake yiwa dakarun gwamnati da na ´yan tawayen kungiyar Lord´s Resistance Army LRA a takaice. A cikin watan agustan bara sassan byiu dake rikici da juna suka amince da shirin tsagita wuta. A cikin shekaru kusan 20 da ta shafe tana gwagwarmaya kungiyar LRA addabi yankin arewacin kasar ta Uganda. ´Yan tawayen sun yi garkuwa da dubban kananan yara da matasa wadanda suka rika tilasta musu shiga aikin soji ko kuma aka rika yin lalata da su.