1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana samun ci-gaba a ƙasar Burma

November 14, 2007
https://p.dw.com/p/CDby
Jakadan MDD na musamman Ibrahin Gambari ya yiwa kwamitin sulhu jawabi bayan ziyarar kwanaki 6 da ya kai a kasar Burma ko Myanmar. Ya fadawa kwamitin sulhun cewa ya gamsu da kyawawan matakan da gwamnatin mulkin sojin kasar ta dauka ciki har da dage dokar hana fita da ta kafa lokacin zanga-zangar kin lamirinta. Hakazalika gwamnatin ta saki mutane da sauran firsinonin siyasa sama da dubu 2 da 700. To sai dai ya ce har yanzu gwamnatin ba ta ba da tabbacin sakin shugabar ´yan adawa Aung San Suu Kyi daga daurin talala da ta shafe shekaru 18 tana ciki ba. ya kuma nuna damuwa dangane da rahotannin keta hakkin bil Adama dake ci-gaba a Burma. Yayin da Gambari ya mayar da hankali kan kyawawan ci-gaba da aka samu a ziyarar sa, shi kuwa jakadan Birtaniya John Sawers cewa yayi takaita zirga-zirga Alh. Gambari ya nunar a fili cewa gwamnatin Burma ba ta cika sharuddan kwamitin sulhu ba.