ana sa ran Turkiya tara yi watsi da kasa da kasa | Labarai | DW | 17.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ana sa ran Turkiya tara yi watsi da kasa da kasa

A yau ne ake sa ran gwamnatin Turkiya zata yi watsi da matsin lamba na kasa da kasa inda zata baiwa dakarunta iznin shiga arewacin Iraqi domin tarwatsa gungun Qurdawa yan tawaye da suka kafa sansaninsu a yankin,kodayake tace ba hari zata kai kann Qurdawan ba.Kasar Amurka wadda abokiyar kawancen Turkiya ce,ta baiyana tsoronta cewa kutsawar sojojin Turkiya arewacin Iraqi zai tarwatsa yankin dake zama daya daga cikin yankuna da ake da sauran zaman lafiya a Iraqi da sauran yankin baki daya.Sai dai kuma sakatare janar na MDD Ban Ki Moon yace babu wata barazana na yaduwar riciki a yankin.