Ana sa ran tattauna batun sakawa Iran takunkumi | Labarai | DW | 05.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana sa ran tattauna batun sakawa Iran takunkumi

A mako mai zuwa ne ake sa ran komitin sulhu na MDD zai fara tattauna batun kafa takunkumin diplomasiya ko na karya tattalin arziki akan kasar Iran,bayan kokarin shawo kann Iran ta dakatar da aiyukanta na nukiliya ya ci tura.

Jakada Emyr Jones Parry yace,kasar Burtaniya zata tattauna tare da sauran membobin komitin daukar mataki karkashin kudirin MDD na 41 .

Karkashin dokar,komitin sulhu yana da ikon lakaba takunkumin diplomasiya kona karya tattalin arzki domin tilsta bin kudirorinta.

A farkon wannan makon sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice,ta sanarda wani taro tsakanin ministocin harkokin wajen manyan kasashen duniya 6 da suka hada da Burtaniya,Faransa,Amurka Sin Rasha da kuma Jamus akan wannan batu.

Babu wani ci gaba da aka samu cikin ganawa kusan sau 4 tsakanin kantoman kula da manufofin wajen Kungiyar Taraiyar Turai Javier Solana da Ali Larijani mai shiga tsakani na Iran.