Ana sa ran Taliban zata sako yan Koriya ta kudu a yau | Labarai | DW | 29.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana sa ran Taliban zata sako yan Koriya ta kudu a yau

Ofishin jakadancin koriya ta kudu da kungiyar Taliban sunce a yau ake sa ran yan kungiyar taliban a Afghanistan zasu sako wasu daga cikin yan kasar Koriya ta kudu 19 da suke garkuwa da su.Kakakin kungiyar Taliban Yousuf Ahmadi ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AFP cewa,zaa sako wani bangare na wadannan mutane amma bai baiyana yawan mutanen ko kuma lokacin da zasu sako su ba.wannan dai ya biyo bayan tattaunawa ce kai tsaye tsakanin jamian diplomasiya na Koriya da wakilan taliban.Koriya ta kudu ta amince ta janye dukkan sojojinta daga Afghanistan zata kuma dakatar da dukkan wasu aiyukan kungiyoyin kirista na yan kasarta a kasar nan zuwa shekara guda.A halinda ake ciki kuma babu wani bayani kann halinda injiniyan Jamus dan shekaru 62 yake ciki,bayan yan bindiga na taliban sun sace shi a watan daya gabata.