1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana koyawa bakin haure sana'oi a Agadez

Tila Amadou
December 12, 2016

Kungiyar kula da bakin haure masu shigowa ko wucewa wasu kasashen Turai wato OIM, ta bullo da wani sabon salon horar da bakin sana'ar hannu don samun dogaro da kawunansu, idan sun koma kasashensu na asali.

https://p.dw.com/p/2RJfD
Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Agadez jiha ce da bakin haure masu tasowa daga kasashen Afrika ke yada zango, kafin su wuce kasar Libiya. Bayan sun dauki lokaci sai su wuce Turai ta barauniyar hanya,inda sukan sha wahala har ta kai su rasa rayukansu. Wannan ya sa kungiyar da ke kula da bakin haure a Agadez ta ke ba su horo a kan sana'oin hannu kafin su wuce kasashen su na asali. Lucien dan Kasar Kamaru wanda ya koyi aikin kira cewa ya yi:

"Da farko an gwada mana irin kayayyakin da ya kamata mu tanada don kira, bayan haka kuma an nuna mana yadda za mu gane zinariya mara gami. An koya mana yadda a ke kira mashi, munduwa da sauransu har na tsawon watanni Biyu".

Lucien ya ce, wannan yunkuri zai taimakawa rayuwarsa ko da ya koma kasarsa Kamaru

."Da zarar na koma kasata Kamaru, zan nemi wata rumfa inda zan kafa makera, in nemi na kaina. Saboda na samu kayan aiki da jari na makera da zan kafa masana'anta ta kaina". 

Bakin Hauren dai sun samu horo daban-daban kan kira da koyon aikin Komfuta da aikin gini da sauransu. Sai dai ayar tambaya a nan ita ce, shin wannan zai taimaka wajen hana bakin hauren fitowa zuwa wasu kasashen Turai ko a'a.?