Ana kai harin ɗaukar fansa akan masallatan ´yan sunni a IraƘi | Labarai | DW | 14.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana kai harin ɗaukar fansa akan masallatan ´yan sunni a IraƘi

Shugabannin mabiya darikar shi´a a Iraqi sun yi kira da a kwantar da hankula bayan wani hari da ake zargin ´yan Al-Qaida da kaiwa, ya lalata hasumiyar masallacin ´yan shi´a dake garin Samarra. An kai harin ne duk da matakan tsaro da ake dauka a gaban masallacin al-Askari. Irin wannan hari da aka kai kan masallacin kimanin watanni 15 da suka wuce ya haddasa mummunan tashe tashen hankula a fadin kasar ta Iraqi. FM Iraqi Nuri al-Maliki da shugaban Amirka GWB sun zargi kungiyar al-Qaida da hannu a harin. Jim kadan bayan fashewar bam din a Samarra, an kai hare haren daukar fansa a kan masallatan ´yan sunni guda 4. A halin da ake ciki gwamnatin Iraqi ta kafa dokar hana fita a Samarra da kuma Bagadaza a wani mataki na shawo kan tashe tashen hankula.