Ana kada kuri′ar zaben shugaban kasar Chadi | Labarai | DW | 10.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana kada kuri'ar zaben shugaban kasar Chadi

Shugaba Idriss Deby na Chadi ya na fuskantar kalubale a zaben shugaban kasa daga 'yan adawa da ke neman kawo karshen mulkinsa na shakaru da dama.

Yanzu haka al'umar kasar Chadi na kada kuri'a domin zaben shugaban kasa, inda 'yan takara da dama ke fafatawa cikin har da Shugaba Idriss Deby da ya shafe fiye da shekaru 25 kan madafun iko, wanda yake neman sabon wa'adin mulki na biyar

Deby dan shekaru 63 wanda yake rike da madafun iko tun shekarar 1990 ke kan gaba da sauran 'yan takara amma akwai yiwuwar zai fuskanci fafatawa mai zafi. Tun bayan gano arzikin man fetur kasar ta Chadi mai mutane milyan 13 da ke yankin tsakiyar Afirka ta samun habakar tattalin arziki gami da taka muhimmiyar rawa tsakanin kasashen yankin.

Zaben kasar ta Chadi ya zo kwanaki bayan fito na fito tsakanin jami'an tsaro da kungiyoyin fararen hula sakamakaon yanda gwamnati ta cafke wasu shugabannin kungiyoyin.