1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana iya soke taimakon EU ga Falasdinawa idan Hamas ta lashe zabe

Babban jami´in kula da harkokin ketare na KTT Javier Solana ya ce idan kungiyar Hamas ta yi nasara a zaben da za´a gudanar a yankunan Falasdinawa a watan gobe kuma ta ki yin watsi da tashe-tashen hankula, to kungiyar EU ka iya daina ba wa hukumar mulkin Falasdinu duk wani taimako. Kungiyar Hamas ta Falasdinawa masu gwagwarmaya da makami, na da hannu a jerin hare haren kunar bakin waken da ake kaiwa Isra´ila wadanda kuma suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan Yahudawa. Kungiyar ta lashe mazabu da dama a zabukan kananan hukumomi da aka gudanar cikin makon jiya a Gabar Yammacin Kogin Jordan. Hamas ta tsayar da ´yan takaran a zaben majalisar dokokin da zai gudana a ranar 25 ga watan janeru mai zuwa. An kiyasce cewar taimakon da EU zata ba Falasdinawa a shekara ta 2006 ya kai euro miliyan 260.