Ana iya fuskantar sabon bala´i a Darfur | Labarai | DW | 09.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana iya fuskantar sabon bala´i a Darfur

MDD ta ce tana fargabar barkewar wani mummunan bala´i a Darfur na yammacin Sudan, idan kungiyar tarayyar Afirka ta ci-gaba da shirin janye sojojin ta daga yankin. Kwamishinan kula da ´yan gudun hijira na MDD Antonio Guterres ya nunar a birnin Geneva cewa yanzu haka babu wani taimako da ake ba wa mutane a sassa daban daban a lardin na Darfur. Ya ce har yanzu ana ci-gaba da tilastawa dubban mutane barin yankin. A karshen wannan wata sojojin kungiyar tarayyar Afirka da ba su da isassun kayan aiki, ke kammala aikinsu a Darfur. A kuma halin da ake ciki gwamnatin Sudan ta saki wani dan jaridar Amirka wanda aka kama a cikin watan agusta bisa zargin yiwa Sudan din leken asiri.