1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zaben ´yan majalisar dokokin Turkiya na gaba da wa´adi

July 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuFq

An fara kada kuri´a a zabukan ´yan majalisar dokokin kasar Turkiya. Jam´iyu 14 da ´yan takara masu zaman kansu 700 ke takarar shiga majalisar dokokin mai kujeru 550. Turkiya ta yanke shawarar gudanar da wannan zabe na gaba da wa´adi a wani yunkuri na rage dambaruwar siyasa a kasar wadda ta samo asali sakamakon adawar da aka nunawa nadin da aak yiwa ministan harkokin waje Abdullahi Gul a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa da FM Recep Tayyip Erdogan ya yi. Binciken jin ra´ayi masu zabe ya nunar da cewa jam´iyar AK ta FM Erdogan zata lashe zaben. Sannan babbar jam´iyar adawa ta Republican zata zo matsayi na biyu. Mutane kimanin miliyan 42 daga cikin al´umar kasar su miliyan 73 suka cancanci kada kuri´a a zaben na yau lahadi.