Ana gudanar da tarukan raye raye a birane 9 na duniya akan sauyin yanayi | Labarai | DW | 07.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana gudanar da tarukan raye raye a birane 9 na duniya akan sauyin yanayi

Ana ci-gaba da gudanar da jerin bukukuwan nan na kade kade da raye raye da aka yiwa lakabi da Live Earth a manya birane 9 na duniya don wayar da jama´a kai game da sauyin yanayi. A birnin Sydney na kasar Australiya aka fara kaddamar da bukukuwan, inda shugabannin ´yan kabilar Aborigins da suka yiwa jikinsu farin fenti suka yiwa jama´a maraba. Tsohon mataimakin shugaban Amirka kuma mai fafatukar kare muhalli Al Gore ya shirya tarukan na kade kade wanda za´a shafe tsawon sa´o´i 24 ana gudanarwa a manyan birane na duniya.

“Al Gore kenan inda ya ke yiwa jama´a godiya da halartar bukukuwan da kuma zama na farko da suka kaddamar da wannan aiki don taimakawa a warware matsalar dumamar yanayi.”

A Tokyo da Shanghai an yi bukukuwan, sai kuma London da Johannesburg da New York da kuma Washington wadanda zasu biyo baya.