Ana garkuwa da bafaranshe guda a Afghanistan | Labarai | DW | 05.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana garkuwa da bafaranshe guda a Afghanistan

Kungiyyar yan taliban dake Afghanistan, ta kara wa´adin bukatar data gabatarwa mahukuntan faransa, kafin sako wasu mutane ciki har da bafaranshe guda da suke garkuwa dasu.

Tsagerun kungiyyar ta Taliban dai na bukatar faranasa, janye sojin ta daga kasar ne ko kuma sako mutanen ta da ake tsare dasu, a matsayin ban gishiri in baka manda.

Yan kungiyyar dai ta Taliban sun shaidar da cewa, zasu jinkirta har zuwa bayan zaben shugaban kasar ta Faransa, kafin nan idan ba a biya musu bukatar tasu ba, su san mataki na gaba da zasu dauka.

A dai gobe lahadi ne kasar ta faransa ke gudanar da zaben na shugaban kasa zagaye na biyu, a tsakanin Nicolas Sarkozy da kuma Seglone Royal.