Ana ganin kiman sojojin Jamus a Afghanistan | Labarai | DW | 31.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ganin kiman sojojin Jamus a Afghanistan

Duk da karuwar hare hare na ´yan Taliban da kuma mummunar arangamar kyamar Amirka da aka yi a Afghanistan, ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung ya nuna goyon bayan sa ga ci-gaba da kasancewar sojojin Jamus a wannan kasa. Ministan ya fadawa tashar telebijin ta Jamus cewa kamar a da har yanzu ma al´umar Afghanistan na ganin rundunar Bundeswehr da kima. To amma ya amsa cewar ana kara samun hauhawar tsamari a arewacin kasar, inda a gobe alhamis Jamus zata karbi ikon jan ragamar rundunar kasa da kasa a wannan yanki. A yau dai daruruwan ´yan tawaye sun kai farmaki a garin Chora dake lardin Urusgan, inda suka fatattaki ´yan sanda daga wannan wuri. Sannan a lardin Zabul dake kudancin kasar kuma mayakan Taliban sun halaka mukaddashin shugaban ´yan sandan yankin.