Ana ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen Iran da Jamus a Berlin | Labarai | DW | 24.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen Iran da Jamus a Berlin

Ministan harkokin wajen Iran Manoucher Mottaki ya fara tattaunawa da takwaran aikin sa na Jamus Frank-Walter Steinmeier a birnin Berlin. Ana wannan ganawa ne yayin da ake cikin halin rashin sanin tabbas game da irin martanin da gwamnati Teheran zata mayar game da tayin taimakon da aka yi mata idan ta dakatar da shirin inganta sinadarin uranium. Kamar yadda aka shirya dazu dazu nan Mottaki ya gana da Mista Steinmeir a gidan gwamnati dake wata unguwar Dahlem amma ba´a a ma´aikatar harkokin waje dake tsakiyar birnin Berlin ba. In an jima za su yi taron manema labarai. Ziyarar ta Mottaki a Berlin ta zo ne a daidai lokacin da Iran take nazarin irin amsar da zata bayar ga tayin taimakon da kasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD da kuma Jamus suka yi mata da nufin warware takaddmar da ake yi game da shirin nukiliyar Iran.