Ana ganawa a birnin Kiev tsakanin shugaba Yuschchenko da Firaminista Yanukovich | Labarai | DW | 26.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ganawa a birnin Kiev tsakanin shugaba Yuschchenko da Firaminista Yanukovich

Shugaban Ukraine Viktor Yuschchenko da FM Viktor Yanukovich na ganawa a Kiev babban birnin kasar da nufin gano bakin zaren warware rikicin siyasar kasar. Fito-na fiton da shugabannin biyu ke yi yayi tsanani a jiya juma´a bayan da shugaban kasa ya ba da umarnin tura karin dakarun ma´aikatar cikin gida zuwa birnin Kiev. Wannan umarnin ya sabawa bukatun ministan cikin gida Vasyl Tsushko. Ana sa ran cewa shugaban da kuma FM zasu yi amfani da taron don tattaunawa akan tsayar da ranar gudanar da zaben ´yan majalisar dokoki. A cikin watan jiya shugaba Yuschchenko ya kafa dokoki biyu don rushe majalisar dokokin tare da kira da a shirya zabe na gaba da wa´adi. A halin da ake ciki FM Yanukovich ya janye adawar da yake nunawa gudanar da zaben na gaba da wa´adi, to amma ya ce ba za´a iya yin zaben gabanin watan oktoba ba.