Ana gab da kakkabe kurkunu a duniya
January 20, 2018Talla
Wani sabon rahoto kan cutar kurkunu ya ce duniya na gab da kawar da cutar kwata-kwata daga doron kasa. Cibiyar da ke yaki da cutar da ke kasar Amirka, ta ce a baya-bayan nan ne dai aka samu mutum 30 da suka kamu da cutar a kasar Habasha wato Ethiopia, bayan shan wani gurbataccen ruwan gulbi.
Kasar Mali da a baya aka samu cutar a cikinta, ta dauki shekaru biyu yanzu ba tare da labarin matsalar ba, kamar yadda ita Sudan ta Kudu ba a samu labarinta ba.
Sama da mutum miliyan uku ne cikin kasashen Afirka da na Asiya, suka yi ta fama da cutar ta kurkunu a cikin gwamman shekaru da suka gabata.