1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fatar samun zaman lafiya mai ɗorewa a Burundi.

June 18, 2006
https://p.dw.com/p/ButO

Gwamnatin Burundi da ɗaya ƙungiyar ’yan tawayen ƙasar, wadda har ila yau take gwagwarmaya da jami’an tsaro, sun amince su tsagaita buɗe wuta tsakaninsu. Yau ne ɓangarorin biyu suka ƙulla wata yarjejeniya a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya, inda suka amince su tsagaita buɗe wa juna wuta har tsawon makwanni biyu, yayin da wakilansu za su ci gaba da tattauna batun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Idan hakan ya samu, to a hukumance dai, za a iya cewa, an kawo ƙarshen yaƙin basasa ke nan a ƙasar, wanda aka fara tun shekarar 1993, bayan kisan gillar da aka yi wa farkon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar. An dai ƙiyasci cewa, fiye da mutane dubu ɗari 3 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru 13 da aka shafe an ata gwabza wannan yaƙin.