Ana fatan sakin Mista Chrobog da iyalinsa a yau ko gobe | Labarai | DW | 30.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana fatan sakin Mista Chrobog da iyalinsa a yau ko gobe

Ana ci-gaba da tuntubar juna da nufin sakin wani tsohon jami´in diplomasiyyar Jamus da iyalinsa da aka yi garkuwa da su. A farkon wannan mako aka sace Jürgen Chrobog da mai dakinsa da kuma ´ya´yansu 3 lokacin da suke ziyarar kasar Yemen. Rahotannin sun ce ´yan bindigan kasar wadanda ke neman a saki ´yan´uwansu biyar da aka daure a kurkuku, suka yi garkuwa da jamusawan. A lokacin da yake ganawa da ´yan jarida a birnin Berlin ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce yana da karfin guiwar cewar za´a sako jamusawan kafin karshen shekara wato yau ke nan ko gobe. Jami´ai a ofishin jakadancin Jamus dake Sanaa, babban birnin Yemen sun ce sun yi magana da mista Chrobog ta wayar tarfo, inda ya tabbatar musu cewar da shi da iyalinsa na cikin koshin lafiya.