1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fargabar komawa ga bawa hamata iska a Sri Lanka

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buo1
Akalla mutane 10 aka kashe sakamakon fadan baya-bayan nan tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawayen Tamil Tigers a kasar Sri Lanka. Fiye da mutane 800 aka halaka a wannan shekarar kadai a tashe tashen hankula a wannan kasa. Yanzu haka dai ana kara fargabar cewa kasar na dab da sake fadawa cikin wani mummunan yakin basasa. To amma wani kakakin gwamnati ya ce kofa a bude take wajen tattauna batun yin sulhu da ´yan tawaye. A halin da ake ciki kasar Norway wadda ta shiga tsakani aka kulla wata yarjejeniyar zaman lafiya a shekara ta 2002, ta fara wani yukuri da nufin ceto wani abin da ya saura daga wannan yarjejeniya.