1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana dab cimma yarjejeniya tsakanin Amirka da Faransa akan rikicin Lebanon

Bayan ja-in-ja game da cimma wani kuduri na bai daya akan rikicin na yankin GTT a kwamitin sulhu na MDD, yanzu an fara ganin alamun kusantar juna tsakanin Amirka da Faransa. Rahotannin baya bayan nan sun nunar da cewa sassan biyu na nazari akan wani kuduri na bai daya tsakaninsu. Kawo yanzu Amirka ta dage kan cewa za´a iya tsagaita wuta ne idan Isra´ila da Lebanon da kuma kungiyar Hisbollah sun cimma wani daidaito na siyasa, yayin da Faransa ta bukaci dakatar da yakin da farko, kafin a shiga wata tattaunawa ta siyasa.