1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da fafatawa tsakanin gwamnati da yan tawayen Tamil Tigers

October 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuhF

A ƙasar Sri lanka ana cigaba da yin ɓarin wuta tsakanin sojojin gwamnati da dana yan awaren Tamil Tigers, yayin da aka shiga rana ta hudu a fafatawar dake gudana a arewaci da kuma gabashin tsibirin. Sojojin Sri lankan sun yi daáwar cewa sun kashe yan tawayen 22 bayan da suka ƙaddamar da farmaki a lardin Batticaloa. Sojin gwamnatin biyu sun sami raunuka. Tun a watan Yulin da ya gabata ɗaruruwan fararen hula tare da sojojin gwamnati dana yan tawaye sun rasa rayukan su a faɗan da ya kaure wanda ya kawo ƙarshen ƙwarya-ƙwaryar shirin zaman lafiyar da aka cimma a shekarar 2002. A ƙarshen wannan watan ne dai aka shirya gudanar da tattaunawa don kawo ƙarshen rikicin na tsawon shekaru 20 to amma babu tabbas ko zaá iya cigaba da wannan shawarwari.