1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da yiwa Masallacin Red Mosque a Islamabad kofar rago

July 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuH9

An yi musayar wuta jefi-jefi a yau laraba a harabar wani masallaci dake Islamabad babban birnin Pakistan wanda jami´an tsaro suka yi kofar rago, kwana daya bayan wata arangama da aka yi a masallacin ta yi sanadiyar mutuwar mutane 16. Da farko dai limamai a masallacin sun bijire da wa´adin da aka ba su na su yi saranda. To sai dai fiye da dalibai 700 sun yi saranda yayin da daruruwan dakarun gwamnati a cikin motocin yaki ke ci-gaba da yiwa harabar masallacin da aka fi sani da Red Mosque kawanya. Duk kokarin da wasu manyan malamai na Pakistan suka yi na shiga tsakani don ganin an kawo karshen wannan fito na fito ya ci-tura.