Ana ci gaba da yakin neman zabe a Nijar
February 1, 2016A Jamhuriyar Nijer 'yan takara na ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa wanda za a yi a jumulce da na 'yan majalisar dokoki a ranar 21 ga watan Fabrairu da muke ciki. Kuma a wani bukin kaddamar da jadawalin aikinsa da yake son yiwa 'yan kasa idan sun sake zaben sa a wanni wa’adi na shekaru biyar, dan takarar jam’iyyar Pnds Tarayya mai mulki Shugaba Issoufou Mahamadou ya ce bai ga abin da zai hana masa shallewa a wani wa’adin mulki ba tun daga zagaye na farko ganin irin yadda shekaru biyar na wa’adin mulkinsa suka samu karbuwa daga al’ummar kasar
"Za mu lashe zaben nan tun a zagaye na farko saboda maimakon jiran har sai an kai ga wa’adi na biyu don kulla kawance tsakaninmu da jam’iyyun siyasa kamar yadda aka saba, to mu mun kulla yarjejeniyar tun a zagayen farko", In ji Shugaban kasa Issoufou Mahamadou dan takarar Jam’iyyar Pnds Tarayya mai mulki a yayin bukin kaddamar da mahimman manufofin da ya saka a gaba idan har jama’a suka sake zaben shi a wani sabon wa’adi na shekaru biyar masu zuwa.
Dan takarar na Jam’iyyar Pnds Tarayya ya bayar da hujjojinsa uku ne yana mai cewar ta dalilinsu ba zai taba faduwa zaben da ke tafe ba a ranar 21 ga wannan watan ganin yadda tun daga farko dan takarar ya kulla yarjejeniya da wasu jam’iyyu kimanin 40 da wasu daga cikinsu suka dakatar da takararsu ta shugabancin kasa, baya ga ayyukan da ya yi da ya ce sun kasance na gari ga 'yan kasa ganin yadda alkawurran da ya dauka na aiki ya zartar da sama da kashi 94 daga cikin dari, kana ga wani sabon alkawalin da ya dauka don kara inganta rayuwar ta 'yan kasar ta jamhuriyar Nijer.
Jam'iyya mai mulki na goyon bayan kalaman shugaban kasa
Kalamun dai na ci gaba da daukar hankali tun daga ranar da shugaban ya furta su. To amma a ganin 'ya 'yan jam’iyyarsa ta Pnds Tarayya shallewa tun daga zagayen na farko da shugaban kasa ya ce ba abin mamaki ba ne. Alhaji Assoumana Malam Issa kakakin Jam’iyyar Pnds Tarayya ne:
Ya ce "To lisafa duk wadannan ayyukan da shugaban kasa ya yi da duk jam’iyyun nan da suka ce tun a zagaye na farko za su kama wa shugaban kasa da talakawan da suka yarda da shugaban kasa da Pnds Tarayya, kenan irin wannan shugaban kasa talakawa sun gano da shi kuma suna alfahari da shi kuma suna bugun gaba da shi da cewar ba su taba samun shugaban kasa kamar shi ba kenan idan har irin wannan shugaban kasar ya dawo ba za su taba cewa idan ya tambayi kuri’arsu su hana shi ba don haka tun zagaye na farko za ya wuce a ranar 21 ga watan febraru"
Ko baya ga 'ya 'yan jam’iyyar ta Pnds Tarayya mai mulki wasu abukanin kawancen jam’iyyar na ci gaba da zuga shugaban kasa da wani kirarin da 'yan adawa suka ce shi ne irinsa na farko da suka taba ji a tarihin siyasar Nijer:
Ya ce "Muna tare da kai ka yi masu kayin tsaye kayin reni kayin da ba a shan fansa tai har su gigice"
'Yan adawa a Nijar sun ce kalaman shugaban kasa na tatsunniya ce
Sai dai tuni abokan hammayar shugaban kasar da suka yanke hukuncin kalubalantar shi suka fara sukar kalaman zarcewar dan takarar tun daga zagayen farko na zabe. Alhaji Tahiru Gimba dan takarar Jam’iyyar Model Ma’aikata ne a zaben shugabancin kasa:
Ya ce "Ai aka ce idan har mai fadi ba ya da hankali ai shi mai saurare ya yi ma kansa hankali. Kenan sai a roki Allah don ya maido da hankalinsu don su san da cewar iko Allah yake bayar da shi kuma yana iya amshe shi yadda ya ga dama don shi ke ba da shi kuma shi ke karbar shi. To idan da Tandja bai fidda man fetur ba ta kaka za’a wani aiki"
Shima dai dan takarar a karkashin inuwar jam'iyyar RSD Gaskiya da ya kasance tare da shugaban a wa’adinsa na farko kuma ya kudri anniyar kalubalantar sa cewa ya yi matakin da shugaban yake son yi a yanzu abu ne da ba’a taba gani ba a Nijer saboda hakan ta kan yiwu ya zamannto lisafin duna kawai. Alhaji Shehu Amadou dan takarar shugaban kasa ne a zaben na wannan shekarar
Ya ce "Wannan ka san dai da akwai kirarin zabe na siyasa kuma kowa yana da irinshi wannnan tunda aka fara siyasa a Nijer zaben shgaban kasa bugu na biyu ake kuma ban ga abin da ya sake a cikin jam’iyyun siyasa ba zuwa yanzu da zai sa a ce hakan za ta kasance a yanzu".
Komi take ci dai fagen siyasar Nijer na kasancewa ko da yauce tamkar mace mai ciki ganin yadda yake bayyana wasu lokutta da ababe irin na ban mamaki wannan fatar na a matsayin wani sabon babi da yekuwar zaben 2016 ta bude da shi a tsakanin 'yan takarar zabe na adawa da masu rinjaye