Ana ci gaba da wata ƙazamar fafatawa tsakanin sojojin Isra’ila da mayaƙan Ƙungiyar Hizbulllahi a kudancin Lebanon. | Labarai | DW | 20.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da wata ƙazamar fafatawa tsakanin sojojin Isra’ila da mayaƙan Ƙungiyar Hizbulllahi a kudancin Lebanon.

Sojojin Isra’ila da suka kutsa cikin kudancin Lebanon na huskanar gagarumar daddagewar da mayaƙan ƙungiyar Hizbullahi a yankin. Wata kafar sojin Isra’ilan dai ta ce hare-haren da dakarun ƙasar suka kai a Lebanon kawo yanzu, sun lalata kusan kashi 50 cikin ɗari na kafofin sojin Hizbulllahin. Amma wasu jami’an ƙungiyar sun musanta wannan ikirarin. Sun kuma ƙaryata wani rahoton da Isra’ilan ta buga na cewa ta lalata wani sansanin ƙarƙashin ƙasa na shugabannin ƙungiyar da bamabamai a birnin Beirut: Ita dai Hizbullahin ta ce, jiragen Isra’ilan sun jefa bam ne kan wani masallacin da ba a gama gina shi bam a tukuna.

Wani rahoton da gidan talabijin nan Al-Jazeera ya bayar ɗazu-ɗazun nan kuma na nuna cewa, sojojin Isra’ila uku sun sheƙa lahira a fafatawar da suka yi yau da mayaƙan ƙungiyar Hizbulllahin a kudancin Lebanon.