1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Brussels

Ibrahim SaniDecember 22, 2007
https://p.dw.com/p/Cf36

Mahukunta a Belgium na ci gaba da tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen birnin Brussels. Shirin na a matsayin rigakafin hasashen kawowa ƙasar hari ne na ta´addanci. An ɗauki wannan mataki ne jim kaɗan bayan jami´an tsaron ƙasar sun sanar da cafke wasu tsageru ne 14, a jiya juma´a. Wata majiya ta ce mutanen na shirin kai hare-hare ne na ta´addanci a ƙasar ta Belgium. Ɗaukar matakin yazo ne a dai dai lokacin da aka ƙaddamar da Gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar ne. An dai shafe tsawon watanni shida ana gwagwarmayar neman madafun iko ne, a tsakanin ma su yaren Flemish da kuma na Faransanci ne a ƙasar.