1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da tattaunawa da ´yan Taliban game da garkuwa da mutane

July 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuFC

´Yan tawayen Taliban dake garkuwa a Afghanistan sun ce bawa gwamnati karin lokaci don bawa wani wakilin gwamnatin birnin Seoul damar shiga cikin tattaunawar da ake yi da nufin sako ´yan KTK 22 da ake garkuwa da su. Kungiyar Taliban dai ta sha nanata cewa zata kashe ma´aikatan agajin idan gwamnatin Afghanistan ba ta sako wasu firsinonin ´yan tawaye 8 ba. A dai halin da ake ciki hukumomin kasar ba su kawad da yiwuwar yin amfani da karfi don ceto mutanen ba, duk da kokarin da masu shiga tsakani ke yi na shawo kan ´yan Taliban a game da makomar ´yan KTK. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen Afghanistan Zemeri Bashary yayi fatan kawo karshen wannan lamari cikin lumana.

Bashary:

“Mun kafa wani kwamiti a lardin Gahzni. Kwamitin ya kunshi shugabannin ´yan sandan Afghanistan da shugabannin wannan lardi da jami´an gwamnatin lardin. Suna aiki ta bangarori da dama. Kuma muna fata abin da muke yi yanzu zai samar da sakamako mai fa´ida.”