1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a Iraqi.

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueM

A ƙasar Iraqi, tahse-tashen hankullan da ke ta yaɗuwa kamar wutar daji sai ƙara haɓaka suke yi. Rahotannin baya-bayan nan da muka samu daga birnin Bagadaza sun ce, wasu ’yan bindingan da ba a gano asalinsu ba tukuna, sun harbe ’yan sanda guda 6 har lahira, sa’annan suka ji wa wasu 10 kuma rauni, a wasu hare-hare guda biyu da suka kai a garin Baquba. Shaidu da suka ga lamarin da idanunsu, sun ce wasu ’yan bindigan sun afka wa tashar ’yan sanda ne a yammacin Baquban, inda kai tsaye suka buɗe musu wuta, sa’annan wani rukunin ’yan tawayen kuma ya kai hari a wani gu inda jami’an tsaro ke binciken motoci kusa da asibitin al-Rahma, wanda ke arewacin garin na Baquba.

A halin da ake ciki dai, wasu majiyoyin rundunar sojin Amirka a Iraqin sun tabbatar da mutuwar sojoji guda biyar na rundunar mayaƙan ruwan ƙasar, a wani ɗauki ba daɗi da suka yi da ’yan yaƙin gwagwarmayar Iraqin a jihar al-Anbar. Hakan dai ya ta da adadin yawan sojojin Amirka da aka kashe a Iraqin a cikin wannan wata na Oktoba zuwa 96, adadin da ya kasance shi ne mafi muni na asarar rayukan sojojin da Amirkan ta taɓa yi a cikin wata ɗaya, tun shekaru 2 da suka wuce.