Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a Iraqi. | Labarai | DW | 13.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a Iraqi.

Har ila yau dai ƙurar rikici ta ƙi lafawa a Iraqi. Rahotannin baya-bayan nan da muka samu sun ce, a ƙalla mutane 35 ne suka sheƙa lahira, sa’annan wasu 60 kuma suka nji rauni, yayin da wani ɗan harin ƙunan baƙin wake ya a da bam, a wata cibiyar ɗaukan ’yan sanda aiki da ke birnin Bagadaza.

A birnin Basra da ke kudancin ƙasar kuma, rahotanni sun ce sojojin Birtaniya 4 ne suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 3 kuma suka ji munanan raunuka, a wani harin da aka kai musu. Kazalika kuma, sojojin Amirka guda 3 ne aka kashe a wani ɗauki ba daɗi a jihar Al Anbar.

A halin da ake ciki dai, rahotannin sun ce Firamiyan Iraqin, Nuri al-Maliki, ya kira ga yi wa gwamnatin ƙasar garambawul, a wani taron bayan shinge da majalisar ƙasar ta gudanar. Sai dai har ila yau, babu ƙarin bayani kan irin garambawul ɗin da al-Malikin ke nufi, ko kuma lokacin da za a aiwatad da shi.