1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a birnin Bagadaza.

November 5, 2006
https://p.dw.com/p/BudL

Ɗazu-ɗazun nan ne kuma mmuka sami rahotannin cewa, an sami ɓarkewar tashe-tashen hankulla a birnin Bagadaza, bayan yanke wa Saddam Hussein hukuncin kisa da wata kotun birnin ta yi. Rahotannin sun ce a ƙalla mutane biyu ne suka sheƙa lahira, sa’annan wasu 8 kuma suka ji rauni, a wani ɗauki ba daɗin da ’yan bindiga suka yi da ’yan sanda a unguwar mabiya ɗariƙar Sunna a arewacin birnin.

A wata sabuwa kuma, hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqin, ta tabbatad da mutuwar wasu sojojinta guda biyu a birnin Bagadazan. Wata sanarwar da hukumar ta bayar ta ce ɗaya sojan ya mutu ne, yayin da abin da ta kira ’yan ta’adda, suka buɗe wa motar sintirin da yake ciki wuta a yammacin birnin. Wani sojan kuma ya mutu ne saboda wasu dalilan da ba ta bnayyana ba, a kan aikinsa a jihar al-Anbar da ke yammacin Iraqin.

Kawo yanzu dai, yawan sojojin Amirkan da suka mutu a Iraqi, tun da suka afka wa ƙasar a cikin shekara ta 2003, ya tashi zuwa dubu 2 da ɗari 8 da 27, inji kamfanin dillancin labaran nan AFP, wanda ke dogaro kan alƙaluman da ma’aikatar tsaron Amirkan wato Pentagon ke bugawa.